Akbar Hashemi Rafsanjani
Akbar Hashemi Rafsanjani (Persian: اکبر هاشمی رفسنجانی, an haife shi a ranar 25 ga watan Agustan 1934 kuma ya mutu a ranar 8 ga watan Janairun 2017) Dan siyasa ne a kasar Iran, marubuci ne kuma daya daga cikin jiga jigan juyin juya hali na kasar kasar ta Iran. Wanda shine shugaban kasa na hudu daga 1989-1997 a shuwagabannin kasar bayan tabbatar da Gwamnatin musulunci. Shine shugaban kwararru masu kafa doka a iran wato Assembly of Experts tun daga 2007 har zuwa 2011 a lokacin da kansa yaji bashida muradin zama a wannan matsayin[1][2]
A cikin shekaru 40 da ya yi yana mulki, Rafsanjani ya tara dimbin madafun iko wanda ya zama kakakin majalisar dokoki, babban kwamanda a lokacin yakin Iran da Iraƙi, sannan ya zabi Ali Khamenei a matsayin shugaban koli na Iran. Matsayinsa mai karfi da iko a kan siyasar Iran ya sa aka ba shi suna Akbar Shah[3][4]
Rafsanjani ya zama shugaban kasar Iran bayan ya lashe zaben 1989. Ya sake yin wani wa’adin mulkin bayan daya kara lashe zaben shekarar 1993. A zaben 2005 ya sake tsayawa takara karo na uku, inda ya zo na daya a zagayen farko na zaben amma a karshe ya sha kaye a hannun abokin hamayyarsa Mahmoud Ahmadinejad a zagaye na biyu na zaben. Shi da iyalinsa sun fuskanci keɓewar siyasa saboda goyon bayan da suka bai wa 'yan adawa a shekarar 2009. Rafsanjani ya kara shiga takarar neman shugabancin ƙasar a shekarar 2013[5] amma Majalisar ta hana shi takara.Da zaben Hassan Rouhani, wanda Rafsanjani ya fito fili ya goyi bayansa, a hankali dangin Rafsanjani sun dawo da martabarsu a siyasance. Rafsanjani ya mutu a cikin 2017, sakamakon bugun zuciya, a wani asibiti a Tehran yana da shekaru 82.[6][7][8] Duk da cewa jami'an gwamnati sun danganta mutuwarsa da bugun zuciya, mutuwarsa ta kwatsam ta sa ake rade-radin cewa an kashe shi. Iyalinsa sun tabbatar da cewa an kashe shi akayi. Wani bincike da aka yi ya nuna cewa jikinsa na dauke da sinadarai masu aman guba wato radioactive.
Farkon Rayuwa da karatu
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Rafsanjani a ranar 25 ga watan Agustan 1934 a ƙauyen Bahreman kusa da birnin Rafsanjan a lardin Kerman, danginsa arziƙi ne manoman pistachio.[9][10] kuma yana da ‘yan’uwa guda bakwai[11]. Mahaifinsa, Mirza Ali Hashemi Behramani, dan kasuwan pistachio ne, daya daga cikin fitattun 'yan kasuwar Kerman. Mahaifiyarsa, Hajie Khanom Mahbibi Hashemi, ta rasu tana da shekaru 90 a duniya a ranar 21 ga Disamban 1995.[12] Daya daga cikin 'yan uwansa, Mohammad Hashemi, shi ne tsohon darektan IRIB.[13]
Cigaban siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Gwagwarmaya kafin Gwamnatin Musulunci
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan tabbatar da Gwamnatin Musulunci
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ In Rafsanjani’s election to key post, Iran moderates see victory Indian Express, 6 September 2007
- ↑ Iran's Rafsanjani Loses Key Post On Assembly Of Experts Radio Free Europe/Radio Liberty, 8 March 2011
- ↑ Wright, Robin (9 January 2017). "Rafsanjani, Iran's Wiliest Revolutionary, Dies". The New Yorker.
- ↑ Ian Black (16 May 2013). "Iran election: Rafsanjani defends decision to stand as his 'national duty'". The Guardian
- ↑ "Iran's Rafsanjani Registers for presidential race". AP. Archived from the original on 11 June 2013. Retrieved 11 May 2013.
- ↑ "Iran's ex-President Rafsanjani dies at 82". 8 January 2017.
- ↑ "Former Iranian President Akbar Hashemi Rafsanjani dead". 8 January 2017.
- ↑ Iran's ex-president Hashemi Rafsanjani dies at 82". 8 January 2017.
- ↑ Ayatollah Akbar Hashemi-Rafsanjani Archived 28 December 2006 at the Wayback Machine from Radio Free Europe
- ↑ "Iran Report: May 9, 2005". Radio Free Europe/Radio Liberty. RadioFreeEurope/RadioLiberty. 11 November 2008.
- ↑ "Rafsanjani's possible return creates a buzz in Tehran". Financial Times. 25 March 2005. Archived from the original on 10 December 2022.
- ↑ "Profile – Hoj. Ali Akbar Rafsanjani". APS Review Gas Market Trends. 19 April 1999. Retrieved 19 June 2013.
- ↑ برخی ناگفته های محمد هاشمی. Tabnak. Archived from the original on 16 August 2017. Retrieved 8 January 2017.