Shawwal
Appearance
Shawwal | |
---|---|
watan kalanda | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | watan Hijira |
Mabiyi | Ramadan |
Ta biyo baya | Dhu al Ki'dah |
Shawwal (Larabci شوال) shine watan goma cikin jerin watannin Musulunci na shekara.
Azumi a watan Shawwal
[gyara sashe | gyara masomin]Ranar farko ta watan shawwal itace ranar Idin karamar sallah. An sunnanta ma musulmai yin azumi na kwana shida a watan Shawwal bayan kammala azumtar dukkannin watan Ramadan. Amma an haramta yin azumi a ranar Idi wato ranar farko ta watan shawwal ko ranar Sallah karama.
Lokuta
[gyara sashe | gyara masomin]Lokuta a watan shawwal daga shekara ta 2016 zuwa 2021
Bayan hijira | Ranar Farko | Ranar Karshe |
---|---|---|
1437 | 06 Yuni 2016 | 03 Ogusta 2016 |
1438 | 26 Yuni 2017 | 23 Yuli 2017 |
1439 | 15 Yuni 2018 | 13 Yuli 2018 |
1440 | 04 Yuni 2019 | 03 Yuli 2019 |
1441 | 24 Mayu 2020 | 21 Yuni 2020 |
1442 | 13
Mayu 2021 |
10 Yuni 2021 |
Kwanakin watan shawwal tsakanin shakarar 2016 da 2021 |
Abubuwan tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]- Ranar 01, Bikin karamar Sallah ko Eid al-Fitr
- Ranar 08, Masarautar Saudiyya ta rusa makabartun Jannatul Baqee da Jannatul Mualla a 1926
- Ranar 13, Haihuwar malamin Sunnah Muhammad Al-Bukhari An haifeshi a shekara ta 194 bayan hijira
- Ranar 22, rasuwar Haji Dost Muhammad Qandhaji, babban malamin Sufanci dan kasar Afganistan
- Ranar 24, Rasuwar Ghulam Farid Sabri da Makbool Ahmed Sabri
- Ranar 25, Shahadar Imam Ja'afar Assadik