Rochas Okorocha
Rochas Okorocha | |||||
---|---|---|---|---|---|
ga Yuni, 2019 - ga Yuni, 2023 ← Hope Uzodimma - Osita Izunaso → District: Imo West
29 Mayu 2011 - 29 Mayu 2019 ← Ikedi Ohakim (mul) - Chukwuemeka Ihedioha → District: Imo West | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Ideato ta Kudu, 22 Satumba 1962 (62 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Tarihin Mutanen Ibo | ||||
Harshen uwa | Harshen, Ibo | ||||
Ƴan uwa | |||||
Abokiyar zama | Nkechi (en) | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Jami'ar, Jos | ||||
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Grand Alliance |
Owelle Rochas Anayo Okorocha (An haife shine a 22 ga watan SatimbaN 1962) Dan kasuwa, mai taimako kuma dan'siyasan Nijeriya ne, Gwamnan Jihar Imo, yayi nasara a zaben Gwamnonin na 6 ga watan Mayu 2011, kuma aka sake zaben sa a karo na biyu a watan Afurilu 11, 2015. Shine yasamar da Gidauniyar Rochas wadda take taimakawa marayu da nakasassu da kuma wasu makarantu na musamman a duk fadin Nijeriya dake ba wa marasa karfi tallafin karatu. Ya fara neman takara ne a karkashin jamiyar All Progressives Grand Alliance (APGA) platform.[1]
Sannan kuma ya dawo All Progressives Congress (APC) a neman sa nabiyu. A dukkanin su, Rochas ya doke, gwamna maici Ikedi Ohakim da kuma mataimakin kakakin majalisar wakilai wato, Hon. Emeka Ihedioha a nasarar sa nabiyu.
A watan Mayun 2022, Rochas Okorocha ya shiga cikin matsalar shari'a. Yayin da ake zarginsa da cin hanci da rashawa, an kama shi a Abuja. A cewar hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa, laifukan da ake zargin an aikata su ne a lokacin da yake rike da mukamin gwamnan jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019. Adadin kudaden da aka wawure zai kai 2.9. Naira biliyan (kimanin dala miliyan bakwai).
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Adimike George, Onitsha (2011-05-07). "Obi hails Okorocha's election". The Nation. Archived from the original on 10 May 2011.