Jump to content

Kofa:Lissafi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kofa:Lissafi
Wikimedia portal (en) Fassara
Lissafi
lissafi

Lissafi ko kuma nazarin ƙidaya wani fanni ne na ilimi wanda yake taimakawa ɗan adam yin ƙidaya da sanin yawan abubuwa da kuma sanin tsarin yadda abubuwa suke idan an cenja su ta wata suffar.[1]

Shi Lissafi wani fannin ilimi ne da ya shafi nazarin ’ya’yan adadi, sarari, tsari, yanayi da sauyi, ana amfani da ilimin lissafi a ɓangarori da yawa kamar; kimiyya, kanikanci, kasuwanci, likitanci da kimiyyar zamantakewa. Amfanin ilimin lissafi a waɗansu lokuta shi ke haifar da sabbin rassa a fannin kamar lissafin ƙididdiga, kuma masana lissafi suna anfani da lissafi tsagwaran sa, ba don wani dalili ba, Ba wani abu da zai iya bayyana maka wannan lissafi ne na amfani ko kuma a’a.

Ana yin lissafi kafin ayi wani abu domin a san mene ne sakamakon abin idan aka aikata wannan ɓangaren na lissafi ana kiransa Kasafi wato ‘statistics’ a turance. A cikin wannan fanni na Kasafi a kan haɗa gamaiyar abubuwa a yi nazari akan sakamakon da za su bayar idan anyi wani abu akan su ta hanyar anfani da alƙalumomin da su ke a cikin su.

Sanin asalin ilimin lissafi abu ne mai wahalar gaske amma an fara ganinlissafai masu wahala ne akusan shekarata 3000 kafin baiyanar Annabi isa (300 MD) a lokacin babila da Misra suka fara lissafin kirge da lissafin awo, Domin haraji , kasuwanci, gine-gine, tsare-tsare da kuma iimin taurari mafi dadewar rubutun da aka samu akan lisafi an same sune a kasa-shen  Mesofotamiya and misra wadanda aka rubuta su a kimani shekaru (2000–1800) kafin haihuwar annabi isah Ya fara faruwa ne a lokacin karni na shida yayin da pathogares(daya daga cikin masanan lissafi na wancen lokacin) da dalibansa suka fara nazarin lissafi amatsayin darasi tareda masana lissafin Girka shekaru 3000 kafin zuwan annabi Isah , Masanin lissafin nan Ecluid shine ya samar da wata hanyar lissafi da akekira da turanci(axiomation). Wanda har yau ana amfani dashi.[2]

  1. https://manhaja.blueprint.ng/asalin-ilimin-lissafi-daga-%C9%97akin-karatu-na-musulunci/
  2. https://www.meteorologiaenred.com/ha/Menene-ilimin-lissafi.html