Jump to content

Fatima Al-Kabbaj

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fatima Al-Kabbaj
Rayuwa
Haihuwa 1932 (92 shekaru)
Sana'a

Fatima Al-Kabbaj ( Tamazight : ⴼⴰⵜⵉⵎⴰ ⵍⵇⴱⴱⴰⵊ) ta kasance daya daga cikin dalibai mata na farko da suka shiga jami'ar al-Qarawiyyin . Daga baya ta zama mace tilo a Majalisar Koli ta Ilimin Addini na Moroko . [1]

Fatima al-Kabbaj ta fara karatunta ne a Dar al-Faqiha, makarantar Islamiyya ta 'yan mata ta Moroko , inda ta koyi karatun Al-Qur'ani. Sannan ta koma Madrasa al-Najah don karatun firamare. Bayan ta kammala karatunta, al-Kabbaj da danginta sun fahimci cewa akwai karancin samun damar karatu ga mata. Bayan tattaunawa da muhawara da dama kan shigar da mata zuwa jami'ar al-Qarawiyyin, al-Kabbaj ta samu damar shiga jami'ar tare da wasu dalibai mata tara. Ta zauna a can na tsawon shekaru goma kuma tayi saukar karatunta a tsakiyar shekara ta dubu daya da dari Tara da hamsin 1950s. [1]

Daga baya ta samar da ilimin sharia ga sarki da iyalansa. Ta yi nuni da cewa mata sun fi bukatar samun damar shiga yaki da jahilci da talakawa fiye da wadanda gwamnati ta nada akan karagar mulki .

An ce gogewarta don ta"ƙalubalanci zato game da damar da matan Morocco suka samu a tarihi na samun ikon addini da kuma motsinsu a fagen ilimin Islama da maza ke mamaye." [1]

  1. 1.0 1.1 1.2 Empty citation (help)