Dokokin nan goma
Appearance
Dokokin nan goma | |
---|---|
Asali | |
Characteristics | |
Description | |
Ɓangaren |
law of Moses (en) Torah (en) Tsohon Alkawari |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Allah ya faɗi dukan waɗannan zantuttuka, ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.
- “Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni.
- “Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa. 5Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina. Amma nakan gwada madawwamiyar ƙaunata ga dubban tsararraki da suke ƙaunata, masu kiyaye dokokina.
- “Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.
- “Tuna da rana Asabar, ka kiyaye ta da tsarki. 9Za ku yi dukan ayyukanku cikin kwana shida, amma rana ta bakwai keɓaɓɓiya ce ga Ubangiji Allahnka. A ranar ba za ka yi kowane irin aiki ba, ko kai, ko 'ya'yanka, ko barorinka, ko dabbobinka, ko kuwa baƙon da yake zaune tare da ku. Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji yakeɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.
- “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
- “Kada ka yi kisankai.
- “Kada ka yi zina.
- “Kada ka yi sata.
- “Kada ka ɓāta sunan maƙwabcinka.
- “Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa.