Abu Abdallah Mohammed II Saadi
Abu Abdallah Mohammed II Saadi | |||
---|---|---|---|
1574 (Gregorian) - 1576 (Gregorian) ← Abdallah al-Ghalib (en) - Abu Marwan Abd al-Malik I Saadi (en) → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 16 century | ||
ƙasa | Moroko | ||
Harshen uwa | Larabci | ||
Mutuwa | Ksar el-Kebir (en) , 4 ga Augusta, 1578 | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Abdallah al-Ghalib | ||
Yara |
view
| ||
Yare | Saadi dynasty (en) | ||
Karatu | |||
Harsuna | Larabci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | sultan (en) | ||
Imani | |||
Addini | Mabiya Sunnah |
Abu Abdallah Mohammed II, Al-Mutawakkil,sau da yawa kawai Abdallah Mohammed (ya mutune a ranar 4 ga watan Agustan shekarar 1578) kuma ya kasance Sarkin Maroko daga shekarar 1574 zuwa shekara ta 1576. Shi ne babban ɗan Abdallah al-Ghalib kuma ya zama Sarkin Musulmi bayan mutuwar mahaifinsa.[ana buƙatar hujja]
Nan da nan bayan ya hau kan gadon sarauta,ya sa aka ƙashe wani ɗan'uwansa kuma aka tsare wani (Mulay en-Naser, gwamnan Tadla).
Kawun Abu Abdallah, Abd al-Malik, wanda,kamar Abdallah al-Ghalib, dan Mohammed ash-Sheikh ne,ya riga ya gudu zuwa Constantinople a daular Usmaniyya a shekarar 1574.[1] Bayan dawowar Ottoman Algeria,Abd al-Malik yayi nasarar shirya rundunarsa, wacce ta kunshi sojojin Ottoman, kuma a shekarar 1576 ya kutsa cikin Maroko ya cinye Fez daga ɗan ɗan'uwansa, a Kame Fez . Yakin farko ya kasance a al-Rukn a cikin ƙasashen Banu waritin, kusa da Fez. A yakin na biyu kusa da Salé (Rabat) a Jandaq al-Rayhan, Abd al-Malik shi ma ya kayar da ɗan ɗan'uwansa. Yaƙi na uku, wanda shi ma Abd al-Malik ya ci nasara, ya gudana a Taroudannt.
Dukansu Abd al-Malik da Abu Abdallah sun mutu bayan shekaru biyu a Yaƙin Alcácer Quibir, a cikin shekarar 1578.A wannan yakin, Abu Abdallah ya yi yakinsa na ƙarshe da kawunsa Abd al-Malik tare da taimakon abokansa na Portugal .
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |