Sanƙarau ko Sanƙaru[1] (Turanci: meningitis)[2] wata cuta ce wacce take rike gabobin dan adam kamar su Kafa, hannu, wuya. Ita cutar anfi saninta a Kasashen Afirk musamman Kasar Najeria, Niger, Cameron, Ghana. Cutar tafi samuwa a lokuta na yanayin zafi. Daya daga cikin cutukan da ba kasafai ake samun maganin su ba sannan an rasa al'umma masu yawa sanayar cutar. Cutar takan taba meninges (wato
shinfidu da suka rufe kwakwalwar Dan Adam)
Cutar na faruwa ne ta sanadiyyar shigar kwayoyin cikin kwakwalwa Koko ruwan dake cikin kwawalwa(Cerebspinal fluid).